top of page

Yadda zaka kiyaye facebok account naka babu wanda zai iya hacking nashi.

Kana so kasan Yadda zaka kiyaye facebok account naka babu wanda zai iya hacking nashi?


Assalamu Alaikum….

Barkan mu da sake saduwa a wannan shiri na biyu, a yau zamu koyi yadda zaka kiyaye facebook account naka neh ka tsare shi ta yadda babu wanda ya isa yayi hacking nashi.

Mutane da dama suna kawo min koken su akan cewa anyi hacking account nasu ma’ana (An sace musu account na facebook), an chanza sunan da suke amfani dashi, wani zakaga daga “Abdurrahman” ya koma “chenesky douglas” hahahaha


No, kuyi hakuri dani dariyar da nayi ba ta ganganci baneh, kawai dai naga sunan ya bani dariya neh, yaushe Abdurrahman ya koma Chenesky Douglas?

Toh wannan kam ba dadi, babu wanda zai so ace anyi Hacking account nashi, musamman hackers na yanzu basuda tausayi bayan sunyi hackinhg account naka zasu share duka friends naka daga list, ta yadda bazaka taba jin dadin Account din ba saboda haka bakada wani zabi wanda ya wuce kayi deleting na account din.

Toh meh zaisa kayi deleting account naka idan akwai yadda zakayi ka kiyaye account din?

GA YADDA AKEYI.

Kayan Aiki.

1. Wayar ka da internet connection (ka kunna data)

2. Facebook lite (yafi sauqin aiki, idan bakada facebook lite kayi downloading a google playstore)


Yanzu bayan ka samu duk abubuwan da muka lissafa a sama, saika bi wannan matakan da zamu bayar a qasa.


1. Bayan ka shiga facebook lite ka danna layuka uku da suke gefen screen din wayarka ta dama kamar yadda ka gani a wannan hoton na qasa.



2. Bayan ka shiga wannan sai ka shiga settings kamar yadda hoto na biyu zai nuna.


3. Idan ka shiga settings kayi qasa kadan zakaga inda aka rubuta "Security and login" ma'anar wannan shine "Tsaro da kuma shiga" (Shiga cikin account). ka danna shi, gashi nan a hoto na gaba.



4. Kamar yadda ka gani a sama, idan ka shiga "Security and login" zkaga bayani a qasa kamar haka "Change your password and take other actions to add more security to your account." ma'ana "ka chanza password naka, sanan ka dauki wasu matakai game da kiyaye accound dinka" toh mu a nan ba chanza password din zamuyi ba, wasu matakan zamu dauka. yanzu bazan cika ku da surutu ba, zamuje kai tsaye zuwa mataki na gaba wanda hoto na gaba yake kawo muku kai tsaye




5. Gashi nan dai kuna gani a sama "Use two factor authentication" wato shi wannan settings din zai baka dama neh ka riqa yin login da wasu kalmomin sirri wanda akafi sani da OTP (one time password), Idan kayi activating settings dinnan toh duk lokacin da kazo login da wata waya da ba taka ba kokuma wayar da baka saba hawan facebook da ita ba, toh koh da ka saka password naka daidai sai sun turo maka wannan password din ta layin ka na waya idan kuma bakada layinka a kusa dakai akwai yadda zakayi zamuyi bayanin shi a nan gaba kadan.

yanzu sai ka danna "Use two factor authentication" ka danna?? toh muje mataki na gaba......


6. A wannan matakin akwai hanyoyi biyu da zaka kunna "two factor Authentication"

  1. Authentication App: Hanya ce da zaka kuna Two-Factor authentication ta hanyar amfani da abunda ake kira "google authenticator" kokuma "Duo Mobile" dayake wannan darasin namu na yau ba dashi zamuyi amfani ba duk da cewa Facebook yafi son muyi amfani dashi, amma Layukan wayoyin mu (MTN, GLO, AIRTEL, 9mobile) sunfi mana sauki kuma sunfi kusa damu fiye da wani "Google authenticator kokuma Duo Mobile" saboda haka zamuyi amfani da hanya ta biyu"

  2. Text Message (SMS): Da wannan zamuyi amfani saboda yafi sauqi kuma yafi sauri, indai layin da kayi registern facebook naka yana kusa dakai shikenan, idan kuma babu layin zaka iya amfani da wani layin naka (Mafi kusa dakai).... yanzu idan ka fahimci abund nake nufi sai ka danna "

  3. " kamar yadda kuke gani a hoton na qasa.



7. Bayan ka danna "Use Text message" kamar yadda kuka gani a hoton sama, abu na gaba shine facebook zai buqaci ka zabi lambar wayar da kakeso kayi amfani da ita a matsayin lambar da Facebook zai rika turo maka "password" da zaka sa da zarar wani ya nemi shiga cikin account naka da wayar da ba taka ba.

Facebook zai fara kawo maka lambar da kayi registan facebook da ita, amma idan kaso zaka chanza ta hanyar danna "Add Phone number" ma'ana Ka saka wata lambar wayar daban. bayan ka shigar da lambar wayar da kake so sai ka danna "Continue"... wannan shi ya kaimu mataki na takwas.



8. Wannan shine mataki na takwas a wannan darasin namu, a nan neh facebook zai buqaci ka saka asalin "Password" (Kalmar sirri) na Facebook naka domin chanza wannan sabon setting da kake so ka saka. sai ka cike Password naka, bayan ka cike sai ka danna "Continue" idan kuma ka manta da asalin password naka sai ka danna "Forgot password".

Bayan ka danna "continue zamuje mataki na gaba.... ka shirya? biyo mu.


9. Mataki na tara: a nan bayan ka saka Password naka zai kawoka wannan shafin kamar yadda kuke gani a hoton na qasa, a nan Facebook zai turo maka wasu lambobi ta layin da ka saka a baya, (Kafin ka saka password naka)...

wannan lambobin neh zakayi amfani dasu ka shigar domin ka tabbatar wa Facebook cewa kaine ka mallaki wannan layin. (Kaga idan ba layinka bane ka saka a baya toh bazaka iya ganin lambobin ba saidai in layin wani yana hannun ka kuma sai kaje kayi amfani da shi toh wannan kuma ka jefa kanka neh a cikin matsala, domin duk lokacin da ka tashi shiga facebook, kokuma kayi sabuwar waya kanaso ka shiga facebook naka, sai an tura mishi password din, kaga kuwan idan baku kusa da juna shikenan sai ka kirashi ka buqaci ya gaya maka Password da facebook suka turo mishi) abunda nake so ince kawai a nan shine;

Ka tabbatar kayi amfani da layin da kayi registan facebook da shi, kokuma layin da kasan cewa naka neh (ma'ana kai ka mallake shi, domin tsaro).

toh ba tare da bata lokaci ba, bayan ka saka lambobin da facebook suka turo maka sai ka danna "continue" idan kuma bakaga lambobin ba sai ka danna "resend code".

zamuje mataki na gaba.....Idan ka saka sai ka fada mana........ No ba saika fada ba, nasan ka saka. hahaha. muje zuwa.


10. Yauwa! kamar yadda kuke gani a hoton a qasa, yanzu ka gama komai, ka kunna "Two-factor authentication" yanzu duk lokacin da ka tashi shiga facebook naka da wata browser "Kama daga asalin Facebook App, Facebook Lite, UCbrowser Faceook, Opera mini, Opera browser, google chrome, Firefox browser, har zuwa Browsers na computer, indai zaka shiga Account naka na facebook da waya, koh browser da baka saba shiga ba, facebook zasu turo maka (One-time-Password) wato kalmar sirri kokuma muce password da zakayi amfani dashi sau daya. domin shiga ciki account naka na facebook. sai kayi amfani da su.


A kiyaye: Sau daya kawai zaka iya amfani dasu idan facebook sun turo (amma zaka iya sawa su turo maka sau dari ma, hahah.

Na cika dariya ko??? yi haquri munzo qarshen darasin yau.

Wani hanzari ba gudu ba;

Mai karatu zaka iya tsayawa a nan idan kaso, amma abubuwan da zasu biyo baya sunada muhimmanci, ina ganin ka tsaya ka karanta su.


TAMBAYOYI DA AMSOSHI.

1. Tambaya: Yaya Zanyi idan Layin da nayi registan "Two-factor Authentication" baya kusa dani?

Amsa: Idan bakaso ka rasa facebook Account naka bayan kayi registan "Two-Factor authentication sai ka danna "Recovery codes" kamar yadda kake gani a hoton nan na qasa:


idan ka danna shi Facebook zasu baka wasu lambobi masu yawa zaka gansu layi-layi sai kayi screenshot din su kkuma ka nemi littafi kusa dakai ka rubuta su.

ga yanayin yadda suke zuwa nan a hoto na qasa.


Kamar yadda ka gani a hoton daya gabata, Facebook za baka "recovery codes" wato lambobi neh masu yawa da zaka iya amfani dasu idan wayarka bata kusa dakai kokuma idan wayarka ta bace, kokuma layin da kayi amfani dashi kokuma ya bace.

A kiyaye: wannan lambobin zaka iya amfani dasu neh sau daya kawai, (ina nufin kowwace code zaka iya amfani da ita neh sau daya idan ba wayarka kusa duk lokacin da ka tashi login, idan kuma ka manta baka rubuta su ba, kokuma bakayi screenshot ba shikenan, kada kazo kace "Mustapha neh yace kayi activating "two Factor Authentication" hahahah.

Kada ka damu koh wayarka bata kusa dakai kuma bakayi screenshot koh ka rubuta wannan lambobin ba, akwai yadda za'ayi Facebook account naka ya dawo. Amma bazamu tattayna wannan darasin a yau ba. ya kamata nima in huta koh?

eh haka neh.


Manufa: da ikon Allah mun cimma manufar kammala wannan karatun, amma dan Allah har yau dai ina rokon mai karatu, kada ka koyi wani darasi a Alfullaty.com bakayi sharing nashi ba, ina nufin ka tura ma wani shima ya amfana. kum ka gayyace shi yazo website din mu yayi liking post namu kuma yayi coment. kaima kada ka manta kayi comment idan ka amfana da abunda ka koya. haka kuma idan akwai gyara kokuma qarin bayani akana bunda muka rubuta za'a iya tuntubar mu kokuma a rubuta a nan qasa. Allah yasa mu dace. Ameen.

Alfullaty.com yake kawo muku wannan shirin tare dani Mustapha Ibrahim.


Tags:

Comments


  • Facebook

©All rights reserved @MFullaty.com

Alfullaty Technologies

NO.9 wambandiggi road, Albarka area maraba, Abuja Nigeria.

Contact

Thanks for contacting me, I will get back to you soon

bottom of page