Website: Yadda ake Neman kudi da shi
- Mustapha Ibrahim
- Jun 3, 2020
- 5 min read
post din daya gabata, munyi bayanin hanyoyi uku da zaka iya Neman kudi a yanar gizo (internet) wato sune.
Website
Facebook
YouTube
Toh zamu dauki website yau muyi bayani akanshi.
Idan baka karanta post din daya gabata ba ka danna nan domin karantawa. Domin bazaka fahimci wannan post din ba saika karantawa Wanda ya gabata.

website
Wato shi website wata babbar hanya CE kokuna muce tana daya daga cikin manyan hanyoyi idan ma batafi kowace hanyar neman kudi a yanar gizo ba, toh babbar hanya ce dai. Cikin mabiya mutane da dams sun bukaci into rubutu akan website da kuma yadda ake bude shi, toh yau burinsu ya cika. A cikin wannan post din akwai:
Menene Ma'anar Website?
Bambancin website da Forum
Banbancin website da blog
Banbancin website da application
Yadda ake bude website
Yadda ake gina website
A darasi na gaba: Yadda ake Neman kudi da website.
Ba tare da bats lokaci ba zamu shiga kai tsaye cikin darasin mu.
Menene website?
Website wani fage ne kokuma gida a yanar gizo (internet) Wanda ake amfani dashi wajen yin abubuwa da dama, abubuwa da suka hada da:
Gidajen hira
Gidajen karatu
Gidajen wasanni
Kasuwanni
Nishadantarwa
Da dai sauransu.....
Yadda ake gane website
Alamomin website guda hudu ne
Na farko: yana zuwa da alamar www. a farko, misali: (www.Alfullaty.com)
Na biyu: Yana zuwa da alaman https:// da farko said ya biyo da www. misali:(https://www.Alfullaty.com)
Na uku: yana zuwa da .com, .in, .me, .us, .you, .(koma menene bayan dot) misali: example.com
Na hudu: yana zuwa da http:// (ba https ba): mafi yawa idan kaga babu (s) a gaban http toh security din bayada kyau, ma'ana website din bayada da security.
Bambancin website da Forum
Dukka forum website ne amma ba duka website bane forum.
Mafi yawan mutane basu San bambancin website da forum ba, forum wajen hira neh. Yanzu mafi yawa basu San cewa Facebook forum baneh, amma idan zaka shiga Facebook ta internet zakaga www.facebook.com kokuma kaga web.facebook.com kokuma wap.facebook.com.
Shi WAP site na waya neh kadai, shi kuma WEB site yafi aiki da kyau idan aka shiga ta computer.
Bambancin website da blog
Dukkan blog website ne amma ba duk website bane blog.
Shi blog waje neh na rubuce-rubuce. Wajen koyar da darussa a rubuce kokuma a bidiyo. Misali yanzu wannan karatun da kakeyi a kan blog kakeyin shi. Ga adireshin blog dinmu nan misali: www.Alfullaty.com/blog
Bambancin website da application
Shi website yanada applications a cikin shi, amma ba'a iya hawan application din sai in akwai data (idan an saying data), kuma sai an bude browser, shi kuma application na waya zaka iya hawan shi kokuma ka Ganshi a wayarka ba tare da internet connection ba, misali. Gallery da kake amfani dashi a wayarka domin duba hotuna da bidiyo, application neh Wanda baya bukatar ka bude internet kafin kayi amfani dashi. Amma akwai Gallery na wannan website din namu Wanda shi kuma sa ka hau kafin ka iya zuwa ka bude shi, zaka iya shiga www.Alfullaty.com domin ganin gallery namu.
Yadda ake bude website
Akwai hanyoyi biyu da zaka iya bude website.
Gina server (zamuyi bayanin as watarana)
Biyan kudi domin ginawa a wata tashar (zamuyi bayanin sa yau)
Idan kanaso ka bude website ta amfani da hanya ta biyu da mukayi bayani a dama sai ka biya kudi, kuma saika rika biyan kudin duk shekara domin sunan website wato (domain name), kamar yadda muka sayi wannan domain din, sai kuma kudin Hosting da zaka rika biya duk wata, kokuma shekara (ya danganta da yadda kakeso kokuma Inda ka sayi host din)
Zamuyi bayanin Domain name da host a kasa.
Domain name:
shine sunan website dinka a yanar gizo, misali yanzu kamar yadda make shiga website dinmu na Alfullaty, ai kaga sunan kamfanin mu neh kuma shine sunan website dinmu toh haka kaima idan kanaso a baka Suna a internet. Misali kanaso ka bude tashar yanar gizo da sunan ka, zaka iya sayen (sunanka.com kokuma sunanka.org koh sunanka.me ko sunanka.ko.UK) koh yaya kakeso zaka iya says.
.com: wannan yafi kyau da kasuwanci
.org: wannan kuma yafi kyau da kungiyoyi
.me: wannan kuma idan kanaso ka says neh da sunan ka toh yafi kyau
Inda ake said a domain name
Dama nasan tunanin ka kenan yanzu, INA zakaje ka sayi domain name?
Manyan hanyoyi da duniya ta yards dasu Wanda amintattu ne a bangaren sayar da domain name da kuma host sune.
WordPress: Shi WordPress yanada Dan tsada kadan, amma yanada inganci sosai kuma idan kanaso ilimin amfani da website kokuma ilimin rubuta code (coding language, Wanda shima zamu karantar dashi a nan Alfullaty.com) toh WordPress yafi koh wanne kyau, amma Lamar yadda na fara, ya Dan fi sauran tsada kuma yafi kyau idan kanaso ilimin coding.
Godaddy: godaddy yafi kowwanne arha, zaka iya sayen domain na tsawon shekara daya ma a Naira dari bakwai (N700)
Kuma yanada security da inganci da tsaro fiye da duk sauran, zaka iya amfani da godaddy idan kanaso ilimin computer da kuma ginin yanar gizo, kuma zaka iya amfani dashi idan ma bakasan ilimin sosai ba, Indai kanada software da zaka gina website dinka shikenan. Kuma Lamar yadda na fada a sama, yafi kowwanne arha.
Wix: a zance mafi gaskiya wix yafi duk sauran amfani, kuma kudin sayen domain a wix ba laifi, amma bai kai godaddy arha ba abunda yasa kuwa shine shi wix yana zuwa da kayan aikin ginin website kyauta, amma godaddy bays zuwa da kayan aiki saidai ka saya kokuma idan kanaso ilimin ginin website ka gina da kanka. Amma wix yanada abubuwan gini sunkai dubu, da zaka iya amfani dasu. Wani abunda zai burgeka shine baka bukatar Sanin ilimin gina website kafin kayi amfani da Wix, koh bakasan komai akan gina website ba zaka iya amfani dashi.
Wanda yafi chanchanta: a gaskiya idan muka duba da kyau six yafi duka sauran amfani kuma yafi kyau, kuma yafi dacewa da kai (mai karatu). Saboda haka idan kanaso ka saying domain kokuma host a wix said ka danna nan
HOST
Kamar yadda mukayi bayanin domain name a matsayin suna, shi kuma host shine wajen ajiya, kamar dai Memory card din wayarka, idan ka saying ways babu memory kamar babu wayar ne domin babu amfani, bazaka iya ajiye hotunan ka, ko bidiyo, ko sauti, ko littafai, kokuma wasu abubuwan masu muhimmanci a cikin wayar ba, saboda bakada memory. Toh haka shima Host, saika sayeshi zaka iya daura hotuna, ko bidiyo a website dinka.
A ina zaka sayi Host?
Zaka iya amfani da hanyoyi uku da mukayi bayani a sama domin sayen host, wato. WordPress, Godaddy, da kuma wix.
Yadda ake gina website
Shi wannan darasin bana kyauta bane, amma zaka iya sayen pack namu a wannan website din, zamu sanar daku idan mun gama gina shafin biyan kudi.
Da wannan ne mukazo karshen darasin my na yau.
Kada ka manta: kayi share (ka tura) wannan post din domin wasu ma su amfana Kamar yadda kaima ka amfana. Mun gode.
Comments