Facebook A yau (1)
- Mustapha Ibrahim
- May 26, 2020
- 7 min read
Barkan mu da sake saduwa yau, saidai kamar yadda kuka gani yau dinnan ba wai zamu kawo muku wani darasi baneh kamar darasin da ya gabata da mukayi akan Yadda ake saita Shafin Facebook domin kasuwanci.

GABATARWA
Meyasa zamu dauki wannan maudu’in (topic) yau?
Dalilai da dama ya jawo hankalina zuwa wannan rubutu game da Facebook a yau da kuma makokmar Al’ummar mu a Facebook. Wato idan ka natsu kayi nazari sosai zaka fahimci vewa ta kowane fuska ana kaimu neh ana barowa, idan nace “Mu” a wannan rubutun a matakin farko ina nufin duk wani dan Nigeria, sai kuma idan ka kara matsawa ina nufin “yan arewa (Arewacin Nigeria), idan nace “Mu” a wannan rubutun ina nufin a Nigerian ta Arewa ma ina nufin Hauswa, wanda mafi yawan cikin nau’in wannan Al’ummar Hausawan Musulmai neh.
A tarihi an san Hausawa akan abunda ya shafi kasuwanci da kuma Addini, wannan abu biyu duk wanda ya taso a Nigeria toh yasan Bahaushe dashi, a kudancin Nigeria kuwa wajen kasuwanci sune Al’ummar da muka sani da ibo (Igbo), toh kamar yadda Igbo suke a kudu wajen kasuwanci haka Hausawa suke a Arewa. Saidai tarihi ya nuna cewa su Hausawa kafin zuwan turawan mulkin mallaka (colonies) Hausawa sunada adiini da kuma kasuwanci. Yanzu haka maganar da Mukeyi Bahaushe ne wanda yafi kowwa kudi a Africa wato “Alico Dangote".
A Arewacin Nigeria Munada manyan malamai kamar yadda mukeda Manyan ‘yan Kasuwa, ba saina lissafa ba amma dai nasan idan na fara lissafi daga
Dan Fodio
Abdullahin Gwandu
Nana Asma’u
Muhammadu Bello Sarkin Musulmi
Sheikh Abubakar Mahmudu Ghumi
Sheik Ja’afar Mahmud Adam
Sheikh Dahiru Bauci
To nasan nayi lissafin malam da duk duniya ta san da zaman su a matsayin malamai kuma 'yan Nigeria neh, a yanzu haka a NIgeria Zamu iya cewa munada makamantan su a ilimi kokuma wanda suka fi su. Amma dai daukaka ta Allah ce. Idan nace zan lissafo Malaman Nigeria wanda sukayi suna a duk duniya baki daya ba a Nigeria bama kadai, toh wallahi zanyi ta Rubutu har in gaji kai kuma zaka sha karatu. Amma menene Alaqar wannan da kuma abubuwan da muke rubutawa?
Inaso mai karatu yayi nazari sosai ya duba makomar samarin mu a yau da yadda suka maida hankali akan Facebook, WhatsApp, Tweeter, Instagram, da sauran kafafen zaman ina hira da manhajoji na abota da hira. Su basu maida hankali sosai da ilimin boko ba, su kuma basu maida hankali da ilimin Kasuwanci yadda akeso ba, hatta wajibin da yake kansu na ilimin Addini ma basu daukeshi a bakin komai ba.
Wannan shine Dalilin da yasa mukyi rubutu a wannan maudu’in (topic).
Abubuwan da suke ciki
Matasa da Facebook
Amfani da lokaci wajen cimma buri.
Mai karatu ya daure ya karanta domin akwai amfani mai yawa a ciki.
1. MATASA DA FACEBOOK
i. Hawa Facebook
Bincike ya nuna A Nigeria kawai akwai mutane da suka mallaki layin waya adadin mutane miliyn dari da ashirin 120 Million cikin al’ummar Nigeria kawai, mafi yawan wannan jama’a suna amfani da layin MTN neh da Kuma Airtel (kamar yadda bincike ya nuna a shekarar 2020)
Ko kasan maiyasa MTN da Airtel sukafi kowwanne daga cikin sauran yawan customers? Saboda a shekarar 2017 MTN d Airtel suka fito da Free Facebook wato “Facebook kyauta” Da babu adadin iya datan da zaka iya amfani da shi a rana daga baya neh abun sai ya chanza salo suka maida shi 20mb kullum. To kasancewa Facebook yayi Arha sosai kuma kusan kowace waya ka saya yanzu tanada Facebook, kuma facebook din yayi arha neh ta wannan layuka guda biyu da farko, kafin Glo da Etisalat/9mobile su fara amfani da facebook na kyauta, shiyasa MTN da Airtel sukafi sauran customers.
Yauwa, yanzu ka fara gano inda muka dosa kuma nasan kanada wannan tambayoyin, dan kawai Facebook yayi Arsha sai matasan Nigeria Musamman Hausawa sufi kowwa a Nigeria Amfani da shi? Eh haka ne, saboda yanzu lalaci da abunda bahaushe yake kira “son Banza” shine ya yawaita a cikin al’ummar mu ta Hausawa kokuma ince Musulmi a wannan bangare na Arewa a Nigeria. Matasan mu suna son Arha sosai, suna son Abubuwan Banza (kamar yadda suke cewa) Yanzu wannan “Free Facebook” da akeyi ya ja mafi yawan mutane kokuma ince mafi yawan matasan Hausawa sun kara samun daman hawan Facebook kyauta indai bazasu kunna hoto ba kokuma bidiyo. Toh zasuyi ta chatting (hira) abunsu har sai sun gaji. A baya idan zamu koma shekarar 2016 zuwa abunda yayi kasa har shekarar 2006 idan muka saka lura sosai zamu fahimci cewa mutane basu faye hawan Facebook kamar yadda suke hawa a yanzu ba (daga 2017 zuwa 2020).
Toh sai kuma ga wata annoba Allah ya jarabci mutane da ita ta “Corona Virus’ wacce ta basu daman zama a gida sosai ba tare da sun fita wajen aiki ba kokuma wajen neman kudi (idan ma akwai sana’ar kenan kokuma aikin, saboda mafi yawan matasan mu a Arewacin Nigeria basuda aikin yi kokuma sana’a, wallahi kuma indai zamu fadi gaskiya abun ya samo asali ne daga lalacin Matasan namu da kuma Zalincin shuwagabanni da gurbataccen shugabanci da muka samu a wannan kasar tamu ta Nigeria.). To haka ba wani abu ya jawo mana ba sai yawan hawan Facebook, What’sapp, da kuma sauran kafafen hira na Zamani. Saboda Corona Virus tazo tasa dole Mutum ya zauna gid, kuma gashi yanada Data sosai a wayarshi, ga Internet connection (damar hawa yanar gizo), ga kuma lokaci ya samu kullum 24/7 (Awa Ashirin da Hudu a sati) baya komai sai cin abinci da Sallah idan akaci sa’a shi mai son ibada ne, sai kuma Bacci. To idan kaine me zakayi a irin wannan yanayi? Ibada? Kokuma cin Abincin? Kokuma Baccin? Musamman ma idan kai gwauro ne. mafi yawan matasn namu gwagware ne. wannan shi yake baka tabbacin cewa samari kokuma matasan mu suna yawan hawa Facebook.
ii. Cikin Facebook
Me sukeyi idan sun shiga cikin Facebook?
Kwarai kuwa da gaske wannan tambaya ce mai matukar muhimmanci kuma abunda yasa zan amsata shine saboda nima matashi ne, da sabon jini na a jiki kuwa, kuma nima a baya nayi irin wannan rayuwar ta yawan hawa Facebook.
Abubuwan da matasa sukeyi yanzu idan sun hau Facebook basu wuce wannan abubuwan ba guda shida (6) kamar haka.
1. Hira da ‘yan mata/samari
2. Bibiyan shafukan mawaka, maraya, da kuma ‘yan film
3. Kalle-kalle na bidio (Videos da ake sawa a Status)
4. Hiran bata lokaci da abokai
5. Bibiyan Shafukan ‘yan matan facebook (timeline)
6. Sada Zumunci da iyaye da kuma abokan Arziki
Kusan yanzu duk wani matashi bahaushe kokoma ince dan arewa, ko dan Nigeria, idan ka bincika mafi yawancin su kasha chasa’in cikin dari (90%) idan suka hau Facebook Abubuwan da sukeyi kenan. Kada ka kara kada kuma ka rage. Zamu tattauna wannan abubuwan da muka lissafa a kasa.
Hira tsakanin yan mata da samari
A gaskiya wani lokacin ina matukar takaicin yadda samarin mu suke mu’amala da ‘yan mata a Facebook da kuma yadda suke yawan hira da su a Facebook, idan kace zakayi bincike a Account (manhaja) ta facebook din mafi yawan matasa/samari zaka samu cewa mafi yawan abokan su a Facebook mata ne, wani ma idan yanada abokai dubu biyar a Facebook to ina mai tabbatar maka dubu hudu mata ne, dubu daya ne kawai maza.
Idan kuma yah au cikin Facebook to jira kawai yake wata budurwa cikin ‘yan matan da yake hira dasu ta hau, da zarar ta hau shikenan sai ka ganshi yana murmushi Kaman wanda aka ba bashin Aure. to me yakawo haka? Dalilai da dama su suka kawo haka, kuma inaso mai karatu ya kara hakuri kadan mun kusa karasa wannan maudu’I (topic). Inaso mai karatu ya natsu sosai ya karanta har zuwa karshe.
Babu mutumin da yake cikin tashin hankali irin gwauron matashi dan Makaranta, wallahi ba kowwa bane zai fahimci asalin abunda nake nufi sai in shima yana cikin irin wannan yanayin ne kokuma ya taba shiga cikin irin wannan halin a rayuwa.
Ka dubi abubuwan da suke cikin Magana ta ya hada abubuwa guda uku (3) (Gwauro, Matashi/saurayi, kuma dan Makaranta).
In dai abun yazo ta bangaren sha’awa ta dabi’ah game da mata to babu wanda yake cikin tashin Hankali irin wannan Mutum. Zanso in tattauna wannan Abubuwan a kasa kamar haka:
GWAURO
Kowwa dai yasan halin da gwauro yake ciki, shi bai samu yayi aure ba kuma yana bukatar aure domin Allah ma ya halicce shi da lafiya kuma ya bashi hankali ya bashi sha’awa, duk lafiyayyen Mutum wanda yake cikin shekarun kuruciya kuma yanada hankalii da kuma cikakkiyar lafiya to yana da sha’awa, idan nace sha’awa a nan ba wai ina nufin sha’awar abinci, ko kudi, kokuma wani abu ba, a’a ina nufin sha’awar jinsin mace. Haka itama mace tanada sha’awar jinsin na miji indai itama tanada cikakkiyar lafiya.
Duk da cewa mun san gwauranaka ba uzuri bane Amma yana daya daga cikin dalilan da yasa Matasa/samari gwagware ko tuzurai suke kasha lafiyar su da lokacin su akan Facebook fiye da ma’aurata. Binciken da mukayi a wannan shekarar ta 2020 ya nuna mana cewa kashi 70 cikin 100 na mutane da suke hawa Facebook wanda basuda Aure be.
Matashi/Saurayi
Matasa/samari sunfi kowa lokaci, saboda kusan mafi yawansu basuda wata sana’a kokuma aikin gwamnati ko na kamfani ko wata ma’aikata da zata dauke musu hankali kokuma ta bata musu lokaci,dayawa daga cikin su sun gama makarantun jami’a, wasu sunyi digiri (degree) wasu kuma har dihiri ta biyu ma sukayi, amma yanayin kasar mu da kuma siyasar kasar mu ya hana mafi yawancin su samun aiki, saboda haka sunada cikakken lokacin hawa Facebook.
Dan Makaranta
Dan Makaranta idan ya kasance shi Gwauro ne, kuma saurayi ne, toh lallai kuwa zaka samu mata suna burge shi, kuma babu yadda ya iya musamman idan makarantar da yake zuwa ta boko ce, kullum indai zai fita zuwa lekcha (lectures) to zai ga wata ta burgeshi, kuma zaiso ya samu lambarta kokuma sunan da take amfani da shi a facebook sboda shi a rayuwarshi bai saba ganin kyawawan mata haka ba indai ba a cikin Makaranta ba sai kuma a TV. Saboda haka zai so su rika yin hira a Facebook ta rika debe mishi kewa (kamar yadda ake cewa). Kuma idan akayi dace itama irinshi ce, itama dama abunda take so kenan, wata ma ta matsu ne tanaso ta bar gidan iyayenta domin taje jami’a ta samu damar yin abunda take so babu wanda yake kalon ta, ta manta cewa Allah wanda ya halicceta yana kallon ta.
To a takaice dai wannnan ma yana daya daga cikin dalilan da matasa kokuma samari maza da mata suke yanawan hira da junan su a facebook.
Mai karatu idan kayi nazari sosai zaka fahimci cewa Matasa/Samari idan sun hau Facebook Farkon Abunda sukeyi shine su duba sakonni (messages) wanda aka turo musu daga abokansu “yan mata kokuma Samari. Zamu shiga zuwa Bangare na biyu da matasa sukeyi a cikin Facebook idan sun Hau. Wanda shine
Bibiyan shafukan ‘yan film, mawaka, da kuma maraya (masu rawa).
Mai karatu sai ayi hakuri, a nan ne zamu dakata sai mun hadu a kasha na biyu na wannan maudu’in na “FACEBOOK A YAU”.
Kada ka manta: kayi “share” (ka tura a Facebook, kokuma Whats’App, ko wani wajen)
Idan akwai wani Karin bayani akan wannan Maudu’i sai ayi tsokaci (comment) a nan kasa.
Ku saurari zuwan kashi na biyu gobe In Allah ya yadda.
Comments