top of page

Manyan hanyoyi guda uku da ake neman kudi a Internet. (darasi na biyu).

Barkan mu da sake saduwa a cikin kasha na biyu a wannan darasin namu na “Kasuwanci a yanar gizo”


Kamar yadda kowwa ya karanta a darasin da ya gabata, yanzu dai munsan kowwa ya fahimci asalin ma’anar “Kasuwanci a yanar gizo” kamar yadda mukayi bayani a darasin da ya gabata, idan baka samu daman karanta darasin da ya gabata ba ka danna nan domin karantawa domin kuwa lallai kana bukatar wannan darasin. Idan baka karanta ba babu yadda za’ayi ka fahimci wannan sabon darasin da zamuyi yanzu a yau dinnan.

Darasin Yau.

Yau zamuyi Magana neh akan “Manyan hanyoyi guda uku da ake neman kudi a Internet (Yanar gizo)”


Wato shi internet wata hanya ce mara adadi da Mutum zai iya neman kudi a cikin ta amma mafi muhimmancin hanyoyin basu wuce hanyoyi uku ba, kada ka kara kada ka rage.


Ga hanyoyin nan kamar haka


1. Website

shafin website kamar www.Alfullaty.com da kake karatu a ciki yanzu, hanya ce da Mutum zai iya neman kudi sosai kuma cikin sauqi (Amma idan yanada ilimi da kuma sanin yadda akeyi).


2. Facebook

Neman kudi ta facebook kadi wata hanya ce itama da ake iya samun kudi sosai cikin sauki, hasali ma neman kudi ta Facebook yafi nema ta website suki, saboda mutane sunfi amfani da Facebook fiye da yadda suke amfani da wasu websites din kamar Alfullaty.com. saidai wani hanzari ba gudu ba shine, A websites (hafin yanar gizo) anfi samun kudi masu yawa duk da cewa hakan yana daukan lokaci sosai kafin a cimma buri kokuma manufa. Kuma amfani da website yafi ‘yanci da iko, kaga misali idan ka mallaki website, babu wanda ya isa yazo y hanaka rubuta abinda kake so ama a Facebook su kansu masu Facebook zasu iya rufe account naka domin kana rubuta, kokuma tura wasu abubuwan da suka saba wa ka’idojin su.


3 Youtube

kowwa dai yasan Youtube ba saina mishi bayanin menene YouTube kokuma yadda ake kallon bidiyo a YouTube ba. Amma mafi yawa zasu bukaci inyi bayanin yadda zasu iya maida YouTube wajen neman kudin, tabbas indai kanada mabiya dayawa (folloers) a YouTube channel naka sosai toh zaka iya samun kudi da shi kuma kudi masu yawa ba kadan ba. Shi Youtube abunda ake bukata kawai shine ka samu mabiya dayawa, Misali idan kanada mabiya Mutum dubu hamsin a Shafinka na YouTube, toh a Nigeria zaka iya samun a qalla Naira dubu dari duk wata, Kada k adamu samun mabiyan abu neh mai sauqi amma zamuyi bayani a Rubutu/darasi nag aba.


Masu karatu kuyi hakuri damu, dayake yau banajin dadin jikina sosai zamu dakata a nan, sai darasi nagaba zamuyi bayanin yadda kowace hanya a cikin wannan hanyoyin guda uku suke aiki. Ku kasance tare damu a www.Alfullaty.com kuma ku saurari darussan mu masu zuwa.


kada ku manta kuyi sharing wannan post din domin wani ma ya amfana kamar yadda kaima ka amfana. Allah yasa mu dace. Ameen.


Ku bibiye mu a darussa na gaba da zasu zo muku duka daga nan Alfullaty.com

Kuyi liking shafin mu na Facebook a nan Danna nan


Darasin mu na gaba: Menene Website (Shafin yanar gizo) da yadda ake neman kudi dashi.

Comments


  • Facebook

©All rights reserved @MFullaty.com

Alfullaty Technologies

NO.9 wambandiggi road, Albarka area maraba, Abuja Nigeria.

Contact

Thanks for contacting me, I will get back to you soon

bottom of page