YADDA AKE HADA XENDER TA WAYA DA KUMA COMPUTER.
- Mustapha Ibrahim
- May 5, 2020
- 6 min read
Updated: May 8, 2020
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Qai.
Kamar yadda kuka sani "Xender" wani "Application" ne na waya wanda zaka iya amfani da shi wajen tura abubuwa masu nauyi daga wayar "Android" zuwa wata "Android" din ta waya, wannan sun hada da files na Video, Audio (Sauti), kokuma applications na waya da dukkan wani abu da zaka iya sharing (Turawa) ta Xender.
.
Toh wannan wani tutorial neh nayi creating wanda zai koyar da mai karatu yanda ake hada alaqar Xender da computer domin tura abubuwa daga waya zuwa computer kokuma daga computer zuwa wayar Android.
ABUBUWAN DA KAKE BUQATA
Wayar Android (Android Phone)
Computer (Laptop kokuma Desktop)
Application na "Xender". idan bakada Application na Xender ka DANNA NAN domin sukewa a wayar ka.
Yauwa, yanzu ka samu duk abunda kake buqata da zamu hada wannan alaqa tsakanin computer da kuma waya ta hanyar Xender.
Da farko dai
Zamuyi muku bayani dalla-dalla a cikin hotuna guda goma masu zuwa, cikin su neh zaku san yadda zakuyi connecting (hada alaqar xender da waya).
Ba tare da bata lokaci ba zamu shiga cikin aikin kai tsaye.
1. Ka duba Application na Xender sai ka bude shi a wayar ka. kamar haka:

2. Bayan ka bude shi a wayar ka sai ka danna alama ta “+” da yake kwanar madubin wayar ka ta dama (screen na xender)

3.Yanzu bayan ka danna shi zakaga ya nuna maka wani screen a wayarka wanda yake baka damar connection da apple, computer (Connect to pc) da kuma sauran “connections” da suke wajen.
Amma mu yanzu zamu dauki “Connect to PC” saboda akanshi neh muke wannan darasin.

1. Yanzu kamar yadda kuke gani a wannan hoton, saiku danna “connect PC” a wayar ku, daga nan zai bude muku wani shafin da zaku iya hada computer da waya. Toh akwai hanyoyi biyu da mutum zai iya yin haka.
i. Ta hanyar amfani da ake kira “Web connect”
ii. Ta hanyar amfani da “Hotspot” (da shi zamuyi amfani saboda yafi sauqi kuma yafi sauri)
Toh bayan ka danna shi zai nuna maka shafin kamar haka.

2. A mataki na biyar abunda zakayi saika danna “Create Hotspot” kamar yadda kuke gani a wannan Hoton na sama. Bayan ka danna “create hotspot” zai kaika mataki na gaba kamar yadda zaku gani a hoto mai zuwa a nan kasa.
KAD KU MANTA: Idan hotspot din wayarku a kunne yake ku kashe shi kafin ku danna “Create hotspot” daga Xender, toh bayan kun danna Create hotspot zakuga wannan shafin kamar haka.

Yauwa. An kusa hada Xender da computer, saura kadan…. Yanzu kamar yadda kuke gani a hoto na sama, idan kuka lura akwai wasu hanyoyi uku da zaka bi kafin ka kulla alaqar Xender da computer ka cikin sauqi ba tare da wani abu ba.
A wannan mataki kana buqatar ka dauko computer ka kunna ta, ka ajiyeta kusa da kai. Sai kabi wannan matakan da zamuyi bayani akansu nan ba da jimawa ba.
Mataki na Farko
ka danna wajen connecting Internet a computer ka kamar haka;

Wannan idan kana amfani da windows 10 kokuma windows 8 kenan. Idan kuma da windows 7 kake amfani kokuma windows Vista, toh zakaga wajen connecting din wifi daidai inda na window 10 yake saika danna shi.
Toh bayan ka dannan wannan “tray” na “wifi wato alamar wifi a computer ka, zakaga “AndroidShare_” kokuma "Xender-Ap" da wasu lambobi” saika danna shi zai kaika inda zakasa password wato “Kalmar sirri” a rubuce a computer kuma abunda zaka gani shine “Enter the Network security key” kokuma “Enter password from router” saika danna “NEXT” bayan ka gama cika password din.
Toh mai karatu zai ita tambayar cewa wane “Password” ake buqatar ya saka? Password din da ake buqatar ka saka shine wanda Xender ya baka a hoton da muka sa kafin wannan shi wato wannan password din ya hada da Harafofi da kuma lambobi.
Toh a haka akeso ka saka shi cikin wannan space na password a computer ka. Zakaga password din kamar haka “23te26y35714udgu” kokuma wani abu makamancin haka. Bayan kasa password din ka danna “next” zai kaika ga mataki na gaba.
Mataki na Biyu; toh a wannan matakin kana bukatar ka bude browser na computer ka (wato software da kake amfani da ita wajen shiga yanar gizo, koh kayi amfani da “Firefox” kokuma “Google chrome” kokuma kayi amfani da “Internet”).
Amma a cikin duka wanna browsers da muka lissafa “Google chrome” kokuma “Firefox” sunfi kyau domin amfani.
Idan bakada browser na google chrome kokuma firefox ka danna nan domin ka sauke su a computer ka, toh ba tare da bata lokaci ba zamu cigaba da connecting Xender da computer, amma ni zanyi amfani da “Firefox” neh (wato Mozilla firefox”)
Kamar yadda kuka gani a hoto mai zuwa;

Toh daga nan zaku lura nayi typing wasu lambobi a cikin inda ake saka website address (wato inda ake ziyarar yanar gizo kamar idan zaka ziyarci www.Alfullaty.com ) toh a ciki neh zaka rubuta wannan lambobi kai tsaye ba tare da ka saka “www.” Ba
A kiyaye: Lambobin za’a danna su ne kai tsaye kawai ba tare da saka komai ba, yadda ka gansu haka zaka rubuta su, kamar nawa da kuke gani cikin hoto na rubuta (192.168.43.132:33455) toh haka zaka rubuta su saika danna “Enter” a keyboard naka (Paipayin rubuttu na computer ka)
Da zarar ka danna “Enter” kayi sauri ka duba wayarka zai kaika shafi mai zuwa kamar haka;

Kamar yadda kuke gani a hoto na sama, idan kuka sa ido da kyau zakuga ya duna wani wuri an rubuta “Accept”: toh shi wannan “accept din ba a computer zaku dannashi ba a waya zaku danna, da zarar kun danna enter zakaga ya nuna maka irin wannan shafin a wayar ka saika danna “Accept” daga wayar taka. Shikenan kayi connecting Xender.
Daga nan mai karatu zai iya tsayawa idan yaso, dama munyi wannan darasi neh yau domin koyan yadda zakayi hada Xender na waya da computer ka
Amma: Idan mai karatu yanaso yasan yadda ake tura abubuwa daga Xender zuwa computer wannan sun hada da Video (bidiyo) kokuma Audio (Sauti) ko hoto, kokuma littafai (pdf) da sauran su, sai ya karanta zuwa karshe.
BAYAN KAYI CONNECTING
(KA KULLA ALAKA)
1. Yadda zaka tura abubuwa daga wayarka zuwa computer: kamar yadda zaku gani a wannan hoton meh zuwa idan ka shiga sashen wayar ka da kakeso ka sauke a computer (ka tura zuwa computer, zaka ga wani dan arrow yana kallon kasa, a kowane hoto kokuma video kokuma file. Saika danna shi, nan take zai shiga computer ka ba tare da dadewa ba.
Idan kana amfani da “Internet download manager” kuma nan take zata bude doming downloading kaya masu nauyi kokuma Video koh hoto kokuma Audio (wato sauti) kamar yadda kuke gani a hoton nan na qasa.

2. Yadda zaka tura abubuwa (Audio,video, littafi, hoto, sauti) daga computer ka zuwa wayar ka:
Shi kuma wannan akwai hanyoyi biyu da zakayi hakan, wanda zasu zo kamar haka.
i. HANYA TA FARKO: Zaka iya amfani da “drag and drop” wato ka kama abunda kakeso ka tura daga computer ka zuwa wayarka ta hanyar amfani da mouse, saika danqo shi da mouse din ka kaishi saman hoton wayar ka saika sake.
Gashi nan a hoto na kasa.

ii. HANYA TA BIYU: zaka iya shiga kowne bangare kamar yadda kuka gani a hoto na sama domin saka abubuwan da suka dace da wajen. Kamar idan kanaso ka tura video daga computer zuwa waya kawai saika zo inda aka nuna Alamar hoto a gefen screen na browser naka saika danna shi, kokum aka danna direct daga asalin screen da aka nuna hoton gida kamar haka:

Kunga dai a wannan hoto na sama idan kuka lura na shiga inda zan iya tura hotuna daga computer zuwa waya neh, toh haka idan zaka tura video kokuma audio, kokuma littafi, koh hoto zakaga an rubuta (Upload Image) idan hoto neh, idan kuma sauti neh zakaga an nuna (Upload Audio) haka idan video neh kokuma littafi (pdf)
Da wannan neh mukazo karshen darasin yau akan yadda zaka kulla alaqar wayar ka da computer ta hanyar xender domin tura abubuwa zuwa computer kokuma daga computer zuwa wayar ka.
Ina fatan wannan darasi ya anfane ni nida ku baki daya, Allah ya sanya mu cikin lada baki daya.
Meh karatu ina rokon Alfarmar wani abu guda daya a wajenka, Dan Allah idan ka amfana da wannan darasi da mukayi yau inaso kaima ka taimaka kayi sharing din wannan rubutun zuwa abokan ka kokuma ‘yan uwan ka domin su amfana. Kamar yadda kaima ka amfana kada ka ajiye amfanin domin ribarka kai kadai. Wasu ma suna buqatar irin wannan darasin da harshen Hausa.
Kamar kuma yadda kuka sani wannan darasi yana nan zuwa da Harshen Turanci.
Kuyi liking facebook page nawa “Baby lawyer” sannan kuma kuyi subscribing a youtube channel din mu “Alfullaty TV” sannan kuma kuyi comment a qasa domin gudun mawa, tambaya, kokuma neman Karin bayani.
MUN GODE
BISSALAM.
Comments