top of page

MEYASA ZAKA BUKACI SANIN KSUWANCI A YANAR GIZO?

DARASI NA BIYU (2)

Kamar yadda kuka gani a darasin farko munyi bayani akan meh ake nufi da kasuwanci a yanar gizo, toh a yau kuma zamu tattauna neh akan Dalilan da yasa kaima zaka bukaci sanin ilimin amfani da yanar gizo wajen kasuwanci kokuma habaka da ci gaba


Dalilai masu yawa suna nuna muhimmancin sanin wannan ilimin. Musamman dai a cikin wannan yanayi da muke ciki, jarabawar da mutane suka shiga ta Corona Virus tasa an kulle kasuwanni, an rufe makarantu, an garqame masallatai da chochi, and hana tafiye-tafiye a manyan hanyoyi, an hana taro na jama’a mai yawa. Toh idan ka lura da irin wannan yanayi na wannan qasar, dama duniya baki daya, zakaga cewa kasuwanni sun durqushe, mafi yawan kasuwanni sun dawo basu aiki, kasuwanni irin Kamfanoni da manya-manyan Ma’aikatu da dai sauran su. Idan zaka sa lura sosai zaka fahimci cewa lallai Makarantu da dama sun dawo Online “Ma’ana a internet” kasuwanni da dama sun dawo amfani da websites

(Kamar www.Alfulaty.com ), haka kuma ma’aikatu da sauran sana’u kala-kala.

Toh idan ka fahimci abunda muke bayani a sama, zaka gane cewa kaima kana bukatar komawa amfani d solution na internet (yanar gizo) ta wannan hanyar ce kaima zaka iya cigaba da kasuwancin ka a yanar gizo ba tare da ka fita waje ba, daga cikin dakin ka. Idan kana daya daga cikin irin wadannan mutanen kana da bukatar sanin yadda ake kasuwanci a yanar gizo;


  1. Kana da karamar kasuwa kokuma sana’a

  2. Ka gama Makaranta ammma baka samu aiki ba

  3. Kai student neh (dalibin Makaranta)

  4. Kana/kina rubuce-rubuce misali kamar Novel kokuma litattafai da kake rubutawa kana saidawa kokuma wanda kake saidawa a internet.

  5. Bakaje Makaranta ba kwata-kwata (boko)

  6. Kana da Makaranta amma dayake corona ta hana ka samun kudi yanzu saboda an rufe makarantu, kana bukatar mayar da makarantar Online (a yanar gizo)

  7. Bakada Makaranta ma, amma kana buqatar bude Makaranta a yanar gizo, kamar wannan makarantar tamu.

  8. Kanaso ka fara saida abubuwa a internet (ka fara saida kayan da kake da su a qasa) ta hanyar internet.

  9. Kanaso ka fara aiki a internet a matsayin dilalli (Affiliate marketing)

  10. Kanaso ka fara aiki matsayin mai talla a internet (Advertisement) kada k adamu nima ina sana’ar talla a yanar gizo kuma tana kawo Alkhairi sosai.

  11. Koyo kakeso kawai kayi domin amfanin kanka.

  12. Kanaso neh ka koya domin kaima ka koyar


Na tabbatar kana daya daga cikin mutanen da muka lissafa a nan sama, dole neh ma kana daya daga cikin su, idan ma baka daya daga cikin su zaka iya shiga duk da haka domin ilimi ba abun wasa dashi baneh, abun a koya neh kuma a iya.


ABUNDA NAKESO DAKU.

Abunda nakeso ka sani idan kana da niyyar shiga cikin wannan tsarin namu bai wuce abubuwa guda uku ba.


1. Haquri

Dole neh kuyi haquri, babu wanda y taba yin mafarkin yayi kudi kuma ya wayi gari kawai ya ganshi yayi kudi, dole neh saida yayi haquri, “Koh kasan cewa na kai shekara takwas ina wannan harkar?” eh, kamar yadda kaji dai nace, shekara takwas! Amma ka duba yanzu ind ya kaini, kuma kaga irin nasarar da na samu a rayuwa, yanzu ina daya daga cikin mutane masu fassara google zuwa harshen Hausa! Kuma ina daya daga cikin masu aiki a “Wix Partners”. Yanzu neh nake cin ribar wannan haqurin da nayi tsawon shekaru 8 da suka wuce. Komai sai da Haquuri. Rayuwa ma sai d haquri.


2. Juriya

saika yi haquri da yawan ayyuka, ina nufin saikay haquri da baccin dare, yanzu akan shirya wannan drussan namu na kasha kwanaki 20 kenan bana samun baccin dare saidai inyi na rana, abubuwa da suka hada da rubuce-rubuce, daukan bidiyo, karance-karance, da kuma bincike. Kaga kuwa ilimin kasuwanci a yanar gizo kadai bai wadatar dani ba saida na kasha dare dayawa na hana idona Bacci kafin wannan darasin yake zuwa muku. Yanzu kai kana ganin zaka iya zaunawa ka karanta littafi mai shafi dari biyu (200 pages) cikin dare daya? Indai har zaka iya toh zaka iya shiga wannan tsarin namu na koyon kasuwanci a yanar gizo. Ba wai ina nufin cewa zamu rika rubuce-rubuce masu yawa baneh A’a, rubutun mu ma idan yayi yawa bazai taba wuce shafi hamsin ba (50 pages). Wannan ina nufin idan mun rubuta dayawa neh ma, amma abunda yasa na kawo misali da shafuka 200 (dari biyu) ina kwatanta Juriyar da ya kamata ace ka samu neh wajen koyon darussan mu.


3. Saka himma

kai ka taba jin labarin wanda yayi kudi ba tare da ya saka kudi ba?

Indai ba zakka za’a baka ba, ko kyauta, sadaka, kokuma kudin sata kokuma na damfara, toh lallai sai an saka kudi kafin a samu kudi, koh kasan cewa domin in gudanar da wannan makarata a duk wata ina kashe abunda bai yi qasa da dubu talatin da biyar ba? (35k/month) duk wata sai na biya wannan kudin, idan ba haka ba bazan samu abunda nake samu a yanzu a wanan kasuwar ba. Toh kaima haka, indai har kanaso ka fara samun Naira dubu dari biyar (500 thousand Naira) duk wata, toh saika shirya kashe Naira dubu dari (100 thousand Naira) duk wata daya. Idan nace zan maka qarya ince zaka samu kudi, kayi kudi, kokum aka zama mai kudi kyauta ba tare da ka kashe koh sisi ba toh nayi maka qarya, duniya ma ba haka take ba, duniya sai Mutum ya kashe kudi kafin zai iya samun kudi, sai ka saka kudi kafin kaima ka samu. Mafi yawan websites kokuma darussa na yanar gizo sunayi wa mutane Alqawarin abunda suma suka san cewa ba tabbas a kai, wasu zasuyi maka alkawarin samun miliyan daya a rana koh baka biya komai ba, amma mu dai a wannan website din babu abinda zamuyi maka alkawari wanda ba haka yake ba, saidai in kai baka sa himma ba.

Toh idan ka fahimci wannan bayanan da nayi a sama zamu iya daukan wannan darussan da kai. Kada in baka tsoro mafi yawan darussan mu kyuta neh indai bazaka iya biyan Naira dari uku a wata ba, kokuma Naira dari biyar a wata (na babban mataki)


Toh da wannan neh muka kawo karshen darasin namu na yau, amma kana bukatar cigaba da karatu idan kana sauri neh dan koyon kasuwanci a yanar gizo ta Facebook.



FACEBOOK A MATSAYIN HANYAR NEMAN KUDI

Shekaru biyar da suka wuce faccebook suka wuce, facebook ya cimma nasarar zama daya daga cikin manyan website kokuma kafar yada bayani ta zamani A duniya, Facebook a yanzu maganar da mukeyi a shekarar 2020 shine babban shafin internet gaba daya a bangaren hira, kokuma yada bayanai na social media. a da, facebook bai wuce kamar website kamar wannan namu ba, amma a yau Mutane biliyoyi suna samun kudi ta hanyar facebook, sun bude kassuwanni da dama a cikin facebook

Akwai Littafi dana rubuta musamman akan amfani da facebook wajen samun kudi masu dimbin yawa, dubu daruruwa. Amma kafin kayi downloading littafin zan so in gaya maka amfanin da yake ciki, kafin ka san nawa zaka biya ya kamata ka fara sanin kai nawa zaka samu.


  1. Yadda ake amfani da "Facebook page" wato shafin facebook wajen samun kudi

  2. Maimakon chat da kake a facebook, zaka iya amfani da lokacin ka ka nema kudi dashi

  3. Dillanci (Affiliate marketing) a facebook.

  4. Facebook Autopilot (har yanzu yana aiki a 2020 saidai ya chanza salon eh kawai)

  5. Amfani da Facebook for business

  6. Tallan hajar ka a facebook

  7. Tallan kasuwar ka a facebook

  8. Tallan Makarantar ka a Facebook

  9. Tallan Kamfanin ka a Facebook

  10. Tallan Kasuwancin ka a facebook (koda pure water kake saidawa kuwa)

  11. Da kuma yadda zaka maida Facebook ya dawo maka ATM

Kamar dai yadda nayi bayani a sama, ba komai ake samu kyauta ba, kaga amfanin da yake cikin wannan littafi n kaima aka so ka mallake shi, amma shi wannan littafin zaka iya cewa ba arha, sai kaga amfanin da yake ciki, kuma sai kaga irin ribar da ka samu kafin zaka zo kana Godiya. Littafin na kasashi kasha biyu neh.

1. Akwai na Hausa

2. Akwai na Turanci

Kuma yanada bangarori guda biyu a cikin sa.

1. Facebook Marketing (Kasuwanci a Facebook)

2. Facebook Digital Marketing (Saida kaya a Facebook).

Bangare na farkon yana bayani neh akan yadda zakayi amfani da facebook koh bakada wani shago, kamfani, Makaranta, kokuma wata sana’a da kake yi a zahiri, (Facebook internet marketing), sai kuma dayan bangaren yana bayani neh akan yadda zaka kawo wa kanka customers dayawa da kuma yadda zaka habaka kasuwancin ka ta hanyar amfani da Facebook (Facebook digital marketing)


NAWA NEH LITTAFIN?

Littafin namu ba wani tsada baneh dashi idan ka duba anfanin da zaka samu a ciki. Amma kuma kafin a saida maka da littafin ana buqatar ka kamala wannan Abubuwan na qasa.

  • Kayi register a website din mu a www.Alfullaty.com

  • Ka sayi babban plan, “MATAKI NA UKU” a website din namu a shafin “Shiga da biya” kokuma “Pricing & Plan”

  • Kayi liking Facebook page namu na Mfullaty

Bayan ka agama wannan matakan uku toh zamu iya saida maka da littafin da sauki

NAWA ZAN BIYA YANZU?

kafin in gaya maka amsar zanso in tambyeka

Nawa kake ganin zaka iya biya domin koyon wani abu da zai iya chanza rayuwar ka?, Naira dubu hamsin? kokuma dubu dari? A'a wallahi koh daya

Toh, dan ka biya miliyoyi dan samun wannan littafi mai muhimmanci haka ba komai baneh saboda abubuwan da suke cikin sa amma mu A Naira dubu biyar kawai (N5,000 only) idan kuma bakayi kowanne daga cikin abubuwan da muka lissafa a sama ba zamu iya saida maka da shi a Naira dubu 7 (N7,000 only).


Kaga kuwa idan dai zaka gwada amfani dashi zaka samu kudi sosai amma kaima idan kana ganin yayi tsada zaka iya bincika Internet kaga nawa suke saida shi? Suna saida shi da tsada sosai wasu ma suna karban har Naira dubu 10, idan yayi arha sosai su sayar maka dashi dubu takwas.

Toh mu kuma a wannan shafin namu muna bayar da shi da yare biyu, Hausa da turanci kuma muna saidashi a Arha, Naira dubu biyar kawai idan ka kamala abubuwan da mukace kayi a sama, idan kuma bakayi ba kaga kuwa zaka biya har Naira dubu bakwai kenan.

Sau daya kawai ake biya, bayan an biya sau daya baza’a sake yin wani biyan ba kuma. Cikin sauqi.


Idan kana ganin kamar duk da haka dai munyi tsada sosai zaka iya bincikawa a google domin ka tabbatar da abunda nake fada.

Babu wanda zai kawo maka irin wannan darussa da sauki haka, kuma cikin yare biyu.

Idan kanaso sai ka Danna nan domin cika form din mu ka biya ta amfani da credit card

(ATM card) kokuma transfer ta banki.


BAYAN MUN TABBATAR DA CEWA KA BIYA.

Zamu turo maka da email tare da ittafin ta email dinka da ka cika lokacin da kake yin register

Mun gode sosai sosai.

Mustapha Ibrahim.


댓글


  • Facebook

©All rights reserved @MFullaty.com

Alfullaty Technologies

NO.9 wambandiggi road, Albarka area maraba, Abuja Nigeria.

Contact

Thanks for contacting me, I will get back to you soon

bottom of page