top of page

Kasuwanci a Facebook a shekarar 2020 (A)



Yadda zakayi amfani da “Facebook for business” wato (Facebook domin kasuwanci)

MENENE FACEBOOK FOR BUSINESS?

Idan dai ka samu damar karanta wannan darasin namu akan yadda Facebook page suke aiki, bamuda bukatar gaya maka ma’anar facebook for Business. Amma domin dai kara samun fahimta a kanshi

Facebook for business wata dam ace da facebook ya kawo domin yin kasuwanci a cikin sa, kamar yadda kasan dai profile na facebook, toh haka shima Facebook for business, shafin facebook ake so ka bude wanda zaka rinka talla, kokuma saida kayan ka a Facebook kokuma muce ta website dinka idan kana da shafin Internet kamar www.Alfullaty.com toh koma bakada shafin Internet zaka iya amfani da Facebook for business ka cimma burin ka ba tare da bata lokaci ba. Kada kaji mamakin bayan k agama karanta wannan darasin ka samu customers dayawa a kasuwancin da kakeyi kokuma abunda kake saidawa. Yana daya daga cikin babban kuskure da mukeyi shine muna kallon dama bazamuyi amfani da ita domin mu samu abunda muke so ba, saidai mu rika yin tambayoyin da basuda amsoshi.

AMFANIN DA ZAKA SAMU IDAN KA GAMA KARANTA WANNAN DARASIN.

  1. Zaka san yadda zakayi tallan kayan ka a Facebok

  2. Zaka san yadda zaka qara samun customers ta hanyar amfani da facebook


ABUBUWAN DA SUKE CIKI

  1. Kashi dalla-dalla (step by step) ta yadda zaka saita Facebook for business.

  2. Kala-kalan posts (types of posts)

  3. Yadda zaka saita tsarin kasuwanci a Facebook cikin mataki bakwai


YADDA ZAKA SAITA FACEBOOK FOR BUSINESS PAGE.

Indai har kanaso ka fara tallan kayan ka toh sai in kanada “Shafin facebook domin kasuwanci” wanda aka fi sani da “Facebook for business page” ga yadda ake kirkiran wannan shafin.

1. BUDE SHAFIN

  • Ka shiga facebook.com/pages/create , amma dole neh ya zama kanad facebook account kafin kai y bude shafin Facebook for business

  • · Ka zabi irin shafin da kakeso ka bude: Facebook zai tambayeka ka zabi irin kasuwar da kakeso ka bude kokuma irin shafin da kakeso ka bude, sai ka zabi “Business” idan ka zabeshi zai kaika mataki na gaba.

  • Enter your business details: a nan neh zaka yi bayanin wace irin kasuwanci ce facebook page dinka zai rika kawo wa mutane (mabiyan ka).


2. SAKA HOTUNA:

Kamar yadda kake saka hotunan ka a profile na Facebook toh haka ma zaka saka hotunan kasuwancin ka da kuma “background” na hotunan a Facebook page din naka


3. BAYANAN SHAFIN KA

Ka danna “Edit page info” saika cike wannan bayanan masu zuwa;

  • Description: Bayanan shafin ka, da abunda kakeyi koh kke saidawa, ba’a so ya wuce harfofi 255

  • Contact information: Bayanin yadda mutane zasu iya neman ka, Lambar waya neh, shafin Internet (website) “website yana da matukar muhimmanci ga kasuwar ka”

  • Wasu bayanan makamantan wannan sun hada lokutan da kake bude shagon ka da lokutan da kake rufewa, dokokin kasuwar taka, kokuma dokokin shafin ka, tsrin saye da sayarwa da sauran su dai.


4. HADA USERNAME (sunan ka a kasuwar, kokuma muce wakilin sunan ka)

“username” na shafin facebook yanada matukar muhimmaci ka danna www.facebook.com/@Username domin hada sabon usernme. Misali ni yanzu ina amfani da www.facebook.com/mbabylawyer kokuma www.facebook.com/Mfullaty

Kadaka manta: wannan username din dashi zakayi amfani a duk lokacin da kakeso ka kawo customer daga shafin ka na internet (website) zuwa shafin ka na facebook, kokuma daga What’App koh daga wani wurin daban indai yana da data kuma zai iya hawa facebook toh zai iya ganin shafin ka, misali yanzu kanaso ka gayyaceni inga shafinka na Facebook, zaka iya gayyata na ka turo min username dinka kamar haka:

www.facebook.com/Sunan_shafin_ka kaga shikenan zan iya zuwa shafin ka inga kasuwancin ka.


5. KA KARA “call to action”: wato shi call to action wani madanni neh (button) da zaka iya dannawa a shafin Mutum domin neman magna dashi kokuma wani abu kamar hakan. Misali zakaga wasu a shafin nasu na facebook sunyi amfani da “Call me” ma’ana wai “A kirani” kokuma “Message me” ma’ana kayi min saqo” a nan neh zaka zabi yaya kafi so kayi alaqa da customers dinka, idan kafi so su kiraka sai ka saka “Call me” idan kuma kafi so su turo maka saqo sai ka danna “Message me”. Idan kanaso ka qara wannan madannin zaka danna

“Add button” neh kawai a wajen sitin shafin naka.


YANZU DA MUKA GM TSARA SHAFIN NAKA NA FACEBOOK YA KAMATA MUJE MATAKI NA GABA, SHINE NAU’I KOKUMA TSARIN POSTING A SHAFIN NAKA.


KALA-KALAN POSTS (type of posts)

A nan neh zamu tattauna irin tsarin post da akafi so kayi amfani dasu wajen creating kokuma wajen yin facebook post domin kasuwncin ka.

1. Zallan Rubutu: akwai post din da zakayi amfani da zallan rubutu wajen yin shi, shi wannan bazaka saka video (bidiyo) kokuma sauti (audio) koh hoto (picture, photo, image) kokuma link ba. Shi wannan ba’a so ka cika yin shi domin a Shafin kasuwanci na facebook baya kawo wasu customers dayawa gaskiya. Amma idan kana yin shi lokaci- zuwa- lokaci toh zaka iya samun customers sosai ta wannan hanyar, misali idan kanada wani offer kokuma ka sauke farashin kayan ka zaka iya amfani dashi domin yafi sauqin karantawa, kuma koh Mutum yana amfani da facebook na kyauta neh (free facebook) zai iya ganin rubutun ka.


2. Amfani da hoto: shi kuma wannan zakayi amfani da hoto neh domin posting din, zi iya kasancewa acikin hoton naka akwai rubutu wanda yake bada labarin kasuwancin ka kokuma abubuwan da kake saidawa, indai zaka iya amfani da wannan damar yadda ya dace toh zaka iya kawo wa kanka customers fiye da yadda kake sammani, saboda mutaneh sunfi saurin duba hoto ma fiye da yadda suke duba rubutu.


3. Video post (bidiyo): amfani da bidiyo zamu iya cewa yafi koh wanne kyau saboda bincike ya nuna cewa mutaneh sunfi kallon bidiyo fiye da yadda suke kallon hoto kokuma karanta rubutu, amma ba’a so bidiyon naka yayi tsayi, anfi so ka tsakaita, Kaman sekan talatin (30 seconds) sun isheka kayi bayanin kasuwancin ka.


4. Link post (post da aka rubuta su a wani waje amma anaso a saka su a shafin Facebook:

Su link post ba’a bukatan sai ka rubuta, kokuma kayi wani sabon bidiyo kokuma hoto, misali dai muce kanada Youtube, ka dora Video naka a youtube kuma kana so ka tura shi zuwa shafin naka na Facebook, abunda akeso kawai shine kaje kayi kofin (copy) na wannan link din bidiyon sai ka dora shi a shafin naka na facebook. Misali: nayi rubutu a shafina na internet kuma inaso in tura shi a Facebook, abunda zanyi kawai shine in kwafo wannan link din misali (( https://www.alfullaty.com/post/meyasa-zaka-bukaci-sanin-ksuwanci-a-yanar-gizo ))

Kaga kamar yadda yayi blue, toh haka link yakeyi a kowane shafin yanar gizo, kawai sai ka danna shi zai kaika zuwa inda ake so ya kaika.

5. Facebook Stories (Status): Facebook basu dade da fara amfani da Status ba tunda facebook suka sayi What’App suka fara amfani dashi a 2017. Toh zaka iya amfani da wannan damar domin dora wasu bayanai na kasuwancin ka idan kana so, zaka iya amfani da bidiyo (video) kokuma Audio, kokum hotuna, amma anfi son kayi amfani da hoto a stories yafi.


Yadda zaka zabi post wanda zaifi kawo maka customers

Yaya za’ayi kasan irin post din da yafi dacewa kayi a shafin ka na kasuwanci?

Mafi girman hanyar da zaka iya yin hakan shine sanin meh customers naka suke so

  • Meh customers naka suke cewa a comment idan sun gama karanta post dinka?

  • Wani bangare neh na post din da kakeyi wanda customers sukafi liking? Kokuma sukafi so?

  • Ya za’ayi ka banbance kanka daga sauran masu gasa da kai a kasuwanci?

Idan har kana iya tambayar kanka wannan tambayoyin da mukayi a sama kuma kana iya amsa su daidai toh kana kusa da samun nasara a abunda ka dosa na kasuwanci a yanar gizo.

Idan kanaso ka bambance kanka da suran masu gasa da kai (masu kasuwanni irin ka) zaka iya faraway da rubuta wani abun da babu wanda yakeda rubutu irinshi a shafin ka, kokum aka fara da saida wani abu wanda babu wanda ya taba saida irin shi kokuma ba’a cika samun irinshi sosai ba. Yanzu kamar misali, darussan da muke kawo muku da Husa zamu iya cewa idan ba mu muka fara bama toh muna daga cikin manyan masu kawo darussa irin wannan da Hausa kuma a yanar gizo, (banda YouTube ma) toh kaga kuwa idan zamu baka misali damu kanmu sai muce mutaneh suna samun wani abu daga garemu wanda basu samu daga wani. Toh hakan shi zaisa mu samu customers sosai inda ace muna saida wsu kaya neh (wanda zamu fara shima nn gaba kadan bada jimawa ba).

Wani hanzari ba gudu ba: kada kaji kunyar tambayan mabiyanka meh suke so? Hakan ba komai zai kawo maka ba sai ci gaba, sanin wani irin bu suke so daga gareka zaisa kasan cewa sun fi son ka fara saida wayoyi fiye da yadda kake saida memory cards da earpiece misali, toh kaga zaka iya yin post musamman domin kaji abubuwan da customers naka suke so, misali zaka iya yin post kamar haka:

“Zamuso sanin ra’ayin ku, da wayar Infinix da Samsung wacce tafi burgeku?”

Toh a nan zakaji mamakin yadda customers zasu cika maka comment akan irin abubuwan da suke so kai kuma daga nan sai ka tabbatar kana kawo musu irin abubuwan da suka ce suna bqata, idan kuma ba saida wasu abubuwa kake ba, kokuma kasuwancin naka a yanar gizo kakeyi kamar irin mutanen da suke saida litattafai a , bakada kasuwa ta zahiri, zaka iya amfani da kalmomi kamar haka Misali:

“Zamuso muji wane littafi kukafi so a cikin littafan da kuka karanta”

ta wannan hanyar zaka samu taimako sosai wajen fahimtar abun da cutomers naka suke so, idan kuma ka gano abunda sukafi so toh kai kum kasan meh zaka maida hankali a kanshi sosai.

Yadda zakayi tsarin kasuwanci a Facebook cikin matakai bakwai (seven steps)

Yanzu tunda ka fahimci kala-kalan post da zaka rika amfani dasu wajen kasuwanci a facebook, yanada kyau ka san wasu dabaru da zakayi domin mabiyan ka su kara yawa, domin kuwa a facebook idan bakada mabiya dayawa kamar bakada komai neh.

1. Sanin irin mutanen da kake hulda dasu

In kanaso mabiyan shafin facebook naka su karu dayawa, kana da bukatar sanin irin mutanen da zakayi mu’amala dasu a facebook

Kayi wa kanka wannnan tambayoyin

  • ‘Yan shekara nawa neh sukafi liking shafin naka?

  • A ina suke rayuwa?

  • Wane irin aiki sukeyi?

  • Meh sukafi so da kuma abunda bazasu so ba?

  • Ta yaya, kuma yaushe da yaushe suke amfani da Facebook?

In dai har zaka iya amsa wannan tambayoyin ina mai tabbatar maka cewa kasuwancin ka zai cigaba kuma zai kai inda baka taba tsammani ba.

Yanzu bari mu duki wani bayani daya akan wannan.

Misali ace kanada mabiya mafi yawa ‘yan shekara hamsin a shafin ka na facebook (your Facebook page), kuma sune sukafi yawa, toh kaga kuwa kawo musu tallan games da finafinai bai dace ba koh kadan, idan kace ta wannan hanyar zaka iya kawo musu abunda suke so toh bazasu taba sayen abunda kake talla ba, domin kuwa shi dattijo dan shekara hamsin (50) baya da lokacin da zai kunna Video games yayi ta bugawa a comfuta kokuma a waya.

Saboda haka wanda sukafi dacewa da shafin naka na faceboook zaka samu basu wuce ‘yan shekara 13-25 ba ma’ana ‘yan shekara sha uku zuwa shekara ashirin da biyar, sune wanda zasufi son shafinka domin sunfi samun lokacin da zasu iya buga game kokuma su kalli fina-finai.

Misali kawai na kawo maka a sama, kuma indai ka fahimci misali na yadda ya dace shikenan bakada bukatan wani abu wanda ya wuce wannan.

Toh idan ka ganeh point dina a sama sosai zaka ganeh cewa bayan wanchan abubuwan kana bukatan sanin wasu abubuwan kamar:

  • Age- shekaru

  • Gender- Maza neh kokuma mata?

  • Education- Karatu (‘yan Makaranta neh?)

  • Relationship status- yaya rayuwar soyayya koh alaqar su da mutane suke? Ma’aurata ne koh kuwa dai basu fara soyayya bama?

  • Location- inda suke rayuwa

  • Language- yaren da suke yi

  • Facebook usage- yawan amfanin su da facebook

  • Past page activity- meh sukafi tattaunawa a kai kokuma muce meh sukafi Magana a kai a Facebook?

Abubuwan dana lissafa a sama suna daya daga cikin mafi muhimmanci wajen kasuwanci a Facebook, sanin su zai taimaka maka sosai wajen fahimtar ci gaban kasuwancin da kakeyi kokuma rashin cigaban ta.

2.Sanin burin da kakeso ka cimma

Akwai takaici sosai kaga kanada likes (mabiya) sosai a shafinka na facebook amma kuma baya kawo maka kudi kokuma customers, kokuma yana kawo customers din amma ba sosai ba kuma yana kawo kudin amma ba sosai ba, yanzu misali, kanada mutane dubu hamsin (50 thousand likes) a shafin ka na Facebook, ya kamata ace shafin yana kawo maka customers Kaman dubu biyar a wata (5,000 customers) kokuma ace a qalla yana kawo maka kudi kamar Naira dubu dari da hamsin (150 thousand Naira) duk wata, idan ba haka ba kuwa toh baya kawo maka abunda kake tsammani kokuma irin customers da kake so.

Kada kaji mamakin zancena haka abun yake, masu shafin Facebook suna samun kudi sosai da shi ta hanyar smun customers kokuma saida abuuwa da sukeyi Online a Internet kokuma shafin nasu na Facbook.


Abubuwan da kowa yake so ya cimma burin sa a shafin nasa na Facebook sun banbanta, wani bukatarshi bata wuce su samu mabiya sosai ba (followes). Idan kanaso ka duba yadda ake samun mabiya sosai a Facebook ka danna nan, amma bamuyi yadda ake samun mabiya sosai a shafin Facebook ba (amma zamuzo muyi rubutu a wannan bangaren shima).


Wani burin shi ya san yadda ake samun mabiya a kan website (shafin Internet), idan kanaso ka samu mabiya sosai a shafin ka na yanar gizo (website) sai ka danna nan, idan kuma kafi so ka maida mabiyanka su dawo customers dinka danna nan.

Toh mucigaba da darasin mu koh? Nasan amsarka itace “eh”


Mu’amala da Mabiya (Followers): Mu’amala da mabiyanka yanada matukar muhimmanci a nasarar kasuwancin ka a Facebook. Wato kasan yadda zaka rika yin posting, Misali muce kanaso kayi tallan takalma (kanada shagon takalma), toh ba’a so ka yawaita tallan takalman naka a facebook. Zamuyi bayanin wannan a cikin kashi 100.


1. Kashi tamanin (80%) na irin posting da kakeyi a shafin naka ya zama suna ilimantarwa neh, kokuma nishadantarwa.

2. Sauran kashi ashirin kuma (remaining 20%) sai ya zama kana posting neh akan tallan hajar

ka, kokuma muce kayan da kake saidawa a Shagon ka (na zahiri) kokuma kayan da kake saidawa a internet kokuma a kan Facebook.


Idan kaso kuma zaka iya amfani da dayan hanyar itace:


Zamu kasa shi kashi uku.

  • Kulla Alaka mai kyau: Ka sani cewa mafi yawan posting da zakayi a shafinka na kasuwanci a facebook domin ka kulla kyakkyawar alaka neh da mabiyanka kokuma customers dinka, idan ka yawaita tallan kayan ka kuma hakan bazai sa ku samu kyakkyawar alaka dasu ba, saboda haka shiyasa ba’a so ka yawaita talla a shafin naka na kasuwanci, idan kuma ka yawaita talla toh akwai matsala, domin kana koran customers naka neh.

  • Kulla yarda (kokuma aminci): Idan kullum aikinka shine talla, yaushe mabiyanka zasu yarda da kai har su sai wani abu daga gareka? Sam babu wanda zaiso ya sayi wani abu daga wajen wanda bai yarda dashi ba, saboda bai san ingancin kayanka ba, saboda haka idan kanaso ka kulla yarda a tsakanin ka da mabiyanka sai kayi abubuwa guda uku.

  1. Kashi daya cikin uku (one third) na abubuwan da kake posting ya zama akan labaran kasuwancin ka neh da kuma yadda kake aiki da kuma nasarar da ka samu “ta hakan neh customers naka zasu yadda dakai”.

  2. Kashi daya kuma cikin biyun da suka rage ya zama kana rubuce-rubuce neh kokuma posting a kan irin yadda kake alaqa da customers naka, Misali zaka iya yin posting Screenshot (hoto) na wani customer naka da yake Godiya akan yadda yake jin dadin kasuwanci da kai, kokuma wani saqo da customer ya turo maka saboda yaji dadin wani abu da ya saya daga wajenka, kokuma irin yadda customers suke yabawa da abunda kake sayarwa kokuma abunda kake kawo musu a Facebook.

  3. Kashin karshe kuma ka rika posting a kan tallan kayanka kokuma hajar ka. Ina mai tabbatar maka idan kabi wannan steps da muka bayar a sama da dukkan bayanan da mukayi toh zaka cimma burin ka sosai a kasuwar yanar gizo (ta hanyar amfani da Facebook for Business page) domin shi wannan shafin da shin neh zaka iya yin kasuwanci a Facebook kuma ka cimma burin ka a shafin Facebook.

Da wannan neh muka kawo karshen posting namu na yau akan amfani da facebook page domin kasuwanci.

Amma wani hanzari ba gudu ba:


Talla:

Akwai content da muka boye sai wanda suka biya

idan kanaso ka san sirrin Facebook da kuma kasuwanci a facebook toh kana bukatar biya kamar haka.

1 Matakin farko: Kyauta neh (shine wannan da ka gama karantawa)

2. Mataki na biyu: Naira dari uku kadai (N300 only) duk wata

3. Mataki na uku: Naira dari biyar kadai (N500 only) duk wata


Idan kuma bazaka iya biyan koh wanne daga ciki ba zaka iya shiga matakin kyauta. Shi kam kyauta neh amma babu wasu muhimman abubuwan da suke cikin sauran matakan.

Shawara: Kana bukatar sanin abubuwan da suke cikin matakin kyauta kafin kaje matakin da zaka biya indai har bakada wani ilimi koh sani game da abunda ya shafi kasuwanci a yanar gizo kokuma kasuwanci a Facebook. Mun gode sosai.

Kada ka manta: Kayi sharing post namu (ka tura shi) wasu ma su karanta, domin kaima kyauta ka karanta. Kada kayi rowa, domin rowa ba kyau.

Комментарии


  • Facebook

©All rights reserved @MFullaty.com

Alfullaty Technologies

NO.9 wambandiggi road, Albarka area maraba, Abuja Nigeria.

Contact

Thanks for contacting me, I will get back to you soon

bottom of page