Hanyoyi biyu da zaka samu Followers (Mabiya) dayawa a facebook. (Da hotuna)
- Mustapha Ibrahim
- May 9, 2020
- 4 min read
Updated: May 10, 2020

GABATARWA
Mafi yawa duk wanda yake hawa Facebook zakaga yanaso ya samu Followers sosai (Ma’ana mabiya) amma bai san wasu hanyoyi zaibi ba domin cimma wannan manufa tasa. Wato akwai hanyoyi masu sauqin gaske da zaka iya bin su domin cimma wannan burin naka, kuma ba wasu hanyoyi baneh masu wuya, hanyoyi neh guda biyu kachal.
Waye bazaiso ya shiga account nashi yaga 10,000 followers ba? Kowwa zaiso hakan domin mabiya Mutum dubu goma zasu sa mutane su yadda da abubuwan da kake rubutawa a facebook, kuma zasu sa mutanen da basu sanka ba su qara sanin kai waye? Hakan kuma zai taimaka maka wajen samun mabiya a zahiri ma ba a facebook kadai ba tunda mutanen da suke hawa facebbok ai mutaneh neh a zahiri, Saboda haka shiyasa wannan darasin yakeda muhimmanci a gareka.
Idan kabi wannan Hanuyoyin ina mai tabbatar maka cewa zaka samu followers da likes (Mutane su bi profile naka, kuma suyi likng post naka. Idan kaci sa’a hada comments).
Ba tare da wani bata lokaci ba bari mu shiga kai tsaye zuwa darasin mu nay au, wanda shine darasi na 3.
DARASI
1. Hanya ta farko: Maida Abokai (friends) su koma followers (mabiya)
Ita wannan hanyar tafi kowwacce sauqi, saidai yafi dacewa ga mutanen da sukeda abokai dayawa a facebook, irin mutanen da sukeda Abokai har 3000-5000 (dubu uku zuwa dubu biyar), Idan bakada abokai dayawa ma zaka iya amfani da ita wannan hanyar amma bazai kai kamar idan kanada abokai dayawa sosai ba.
Kayan aiki:
i. Facebook lite
ii. Ka kunna data a wayar ka
iii. Kana da abokai masu yawa a facebook.
Idan ka hada duka wannan kayan aiki sai mu fara.
1. Ka shiga facebook lite, bayan ka shiga sai ka danna layuka uku da suke gefen screen naka ta sama. saika shiga "Setting" kamar yadda kake gani a hoto mai zuwa.

2. Bayan ka shiga “settings” sai kaje qasa kadan zakaga inda aka rubuta “Privacy settings” saika danna wajen. Gashi nan a hoto mai zuwa.

3. Bayan ka shiga “privacy Settings” zai kawoka Screen wani screen sai kaje qasa kadan a cikin screen din wayar ka zakaga inda aka rubuta “who can send you friend requests?” ma’ana “Su waye zasu iya turo maka da neman abota?’ (friend request).
gashi nan a hton da zaku gani a qasa.

4. Yauwa, bayan ka shiga zakaga ya kawo maka zabi guda biyu, cewa ka zabi irin mutanen da kakeso su rinka turo maka friend request (Neman abota).
i. Everyone (Ma’ana, kowwa ma zai iya turo maka friend request)
ii. Friends of Friends (Ma’ana abokanayen abokan ka neh kadai zasu iya turo maka sakon neman abota)
Toh a nan saika chanza shi ka maidashi “Everyone” ma’ana “Kowwa ma zai iya turo maka da saqon neman kulla abota” kamar yadda kuke gani a wannan hoton mai zuwa.

5. Bayan ka chanza ka maida shi “Everyone” kamar yadda ka gani a sama akwai abu daya da akeso kayi, shine koh mutane sun turo maka friend request kada kayi accepting idan ba ya zama dole ba. Kuma kada kayi deleting (kada ka share friend request din) ka barshi kawai haka nan, da kanshi zai juye ya dawo “Follower” (Mabiyi) zai iya ganin duk abunda kayi posting a facebook kuma zai iya hira dakai ta messenger, duk abunda aboki yakeyi shima zaiyi dakai, kaga anan ka samu riba biyu.
i. Kuna abotar ku kuma kuna hira (chatting)
ii. Kuma yana following naka (Mabiyin ka).
Kamar yadda kuke gani a hoto na qasa, yanzu haka inada Friend Request (wanda mutane suka turo min sun kai saba’in da tara) amma cikin mutaneh 79 dinnan banyi accepting koh guda daya ba, toh a haka kuma Facebook zai maidasu duka (79) din zasu koma mabiya na a facebook.
Kunga abunda nake nufi a wannan hoton na qasa.

Kamar yadda kuke gani a hoton da yake sama, kusan mutane 80 neh suka turo min Friend Request (Neman Abota) amma duka banyi Accepting ba. Hakan baya nufin wai na raina su kokuma na wulakanta su, a’a. Babu abunda bazamuyi dasu ba, wasu dayawa daga cikinsu yanzu haka muna hira (chatting) kuma munayin duk abunda abokai sukeyi (Amma dukan su kuma mabiyana neh) kamar dai yadda abun yake a zahiri a rayuwa, Zaka iya hira da mabiyan ka kamar yadda zakayi da abokan ka.
6. Toh bayan ka maida shi “everyone” kamar yadda ka gani a hoton sama, abunda ake buqata shine ka tabbatar kanayin post mai ma’ana a facebook, wanda mutaneh zasuyi liking har ma suyi maka comment, saika dauki wani maudu’I (topic) da zaka rika yin Magana akansa a facebook, idan kaso zaka iya daukan topics da mutane sukafi so. Mafi yawan mutane sunfi son topics da suka hada da.
i. Barkwanci (Funny posts)
ii. Relationship (soyayya da abunda ya shafi zamantakewa)
iii. Addini
iv. Siyasa
v. Rayuwa
vi. Da kuma Shawari. (Advise).
Zaka iya daukan kowwanne daga cikin wannan kayi rubutu a kai, haka zai taimaka maka wajen samun followers (Mabiya) sosai a Facebook.
Wani Hanzari ba gudu ba: Ka tabbatar duk lokacin da zakayi rubutu a Facebook, ka tabbatar ka sakashi a “Public” kada ka maidashi “Only me, kokuma Friends, kokuma Friends of friends”
Wannan duk zai ja maka neh koh kayi rubutun bazai je koh ina ba. Saboda idan ka saka “Only me” kai kadai neh zakaga post dinka, saboda haka koh kayi posting babu wanda zai gani, balle ya turo maka friend request, balle ma har ya dawo ya zama mabiyin ka (Follower). Haka ma idan ka saka shi a matsayin “Friends”, abokanan ka neh kadai zasu iya ganin rubutun ka. Haka kuma idan ka saka shi a matsayin Friends of friends.
Abu dai mafi muhimmanci da nakeso ka ganeh a nan shine duk lokacin da zakayi rubutu ka tabbatar ka sashi a matsayin “Public” ta yadda kowwa da kowwa zai ga rubutun ka.
Gashi nan a hoto mai zuwa kamar haka.

Alhamdu lillahi, a nan neh muka kawo qarshen wannan darasin namu na yau. Allah yasa mu dace.
Kada a manta: Har kullum dai ina qara rokon ka (Kai mai karatu) idan ka amfana da wannan darasin nawa kayi Share nashi zuwa abokanai da ‘yan uwa domin suma su amfana kamar yadda ka amfana, shi ilimi ba’a boyeshi, kamar yadda kaima ka sameshi a kyauta, kaima ka sanar da wani a kyauta mana, minti 1 kachal yayi yawa zakayi share (zaka tura wa abokan ka) wannan darasin namu.
DARASI NA GABA; Darashi nag aba zamuyi Magana akan Hacking na Facebook (Facebook hack) kuma shima da yaren hausa.
Abubuwa Uku da nake bukatan kayi:
1. kayi share na post dinnan
2. Ka bibiye mu www.Alfullaty.com
3. Sannan Idan mun kawo muku YouTube channel shima kad ku manta kuyi Subscribing.
コメント