Gabatarwa game da abunda ya shafi kasuwanci a internet (a yanar gizo) kashi na 1.
- Mustapha Ibrahim
- May 12, 2020
- 4 min read

Kasuwanci a yanar gizo kashi na daya.
Barkan mu da sake saduwa a wannan darasi.
kamar yadda kuke gani yau zamu fara sabon darasi game da abunda ya shafi kasuwanci a yanar gizo ma'ana (Online or internet marketing) amma dayake yau zamu kaddamar da shi, toh zamu taqaita kwarai da gaske.
Menene ake kira Digital Marketing?
wato shi online or internet marketting (kokuma muce kauwanci a yanar gizo) hanya ce mafi sauqi da zaka iya kasuwanci a gida ba sai wani ya ganka ba, ba sai ka fita ka tafi kasuwa ba, kokuma ka dauki kayan sayarwa a hannun ka ka sayar ba,baya bukatan koh daya daga cikin abubuwan da muka lissafa. wato dai kamar muce kana gida a zaune daga dakinka zaka iya samun kudi ta hanyar "Kasuwanci a yanar gizo" kada ka damu, yanzu haka wani yana tunanin toh wa zai bani kudin? kuma ta yaya zan fara wannan kasuwanci? gaskiya tambayoyin ka abubuwa neh masu muhimmanci kuma ababen dubawa.
Amma kuma tambayoyinka suna nuna alamar kamar rashin yarda kokuma mamakin yadda wannan abu zai kasance.
A takaice dai idan kasan meh ake kira da "internet or online marketing" toh bakada bukatar shan wuya kokuma wani abu makamancin wuya wurin fahimtar cewa ba abu baneh wanda za'ace bazai yiu ba.
Eh, tabbas mafi yawan mutane sunada shakku kokuma ince suna kokwanton ta yaya mutum zai iya samun kudi kawai daga danna computer hahaha. (Allah ya jiqan ka malam bahaushe) amma amsar tambayar ka mai sauqi ce. saidai zanso in maka wata tambaya kafin in amsa wannan tambaya taka.
kai ka taba ganin inda mutum ya samu kudi bai sha wuya ba?
Akaramakallahu ai indai mutum neman kudin yayi kuma ya samu ina mai tabbatar maka ya sha wuya, koh meh yakeyi ma kuwa. bazaka taba sanin irin wahalar da wasu suke kafin su samu kudi ba saika shiga cikin irin gwagwarmayar da suke yi. toh idan ka fahimci cewa ba danna computer kawai sukeyi suke samun kudi ba toh zaka ganeh cewa ashe dai suma suna shan wuya kafin su samu kudi ta hanyar Internet (wato yanar gizo)
amma saidai kada maganata ta sare maka quiwa, ba bau baneh mai wuya sosai indai har ka shirya da gaske kuma kasan yadda akeyi.
Hanyoyin da zaka iya samun kudi kokuma muce kayi kasuwanci a internet (Yanar gizo)
1. Content Marketing: a hausance kuma Abubuwan Sayarwa
wato it wannan hanyar zaka riqa yin kayan sayarwa neh ta internet kamar littafai, bidiyo mai amfani (Kamar wanda mukeyi na darusa) da kuma sauran abubuwa irin su wakoki da dai sauran su da zaka sayar wa customers naka online (Musamman idan kanada website kamar Alfullaty.com)
2. Social Media Marketing: Ma'ana Kasuwanci a kafofin saduwa na yanar gizo
Wannan ma wata muhimmiyar hanya ce da zaka iya samun kudi a online (Internet).
koh ka taba tunanin yadda kake bata lokacin ka a online kana chatting da mutane haka nan kuma babu wanda yake biyanka?
toh meh zai hana kayi amfani da lokacin ka ka cimma burin ka ta hanyar ,aida lokacin ka kudin abincin ka online? zaka iya amfani da Facebook Page zalla, Facebook groups, what'app business app, da makamantan su, akwai Applications sunfi dubu a internet domin taimakawa wajen kasuwanci a internet amma kadan neh daga cikin su na gaskiya.
duk da haka kasuwanci a irin wannan kafa tanada riba mai yawa, amma saika jure.
3. Pay Per Click (PPC): da hausa kuma zamu iya kiranshi "Biya duk lokacin da aka danna"
yes! dama ina jiran ka tambaya neh kawai, duk lokacin da aka danna meh?
Amsa: Duk lokacin da aka danna wata talla (Advert) da kasa awebsite naka, kokuma a youtube Channel naka, kokuma Facebook, koh Whats'App kokuma makamntan haka. Koh kasan cewa idan kanada mutum 50000 (Dubu hamsin) a Youtube naka zaka iya samun Naira 5000 (Dubu dari biyar) duk wata?! kwarai kuwa kudi neh mai yawa amma kada kace bazai yiu ba, shi yafi komai sauqi.
Kai dai kayi fatan samun Subscribers a Youtube naka kawai
4. Affiliate Marketing: a Hausa kuma zamu iya kiran shi "Kasuwancin Dillanci"
Ita wannan hanya tanada sauqi, kai baka da buqatan wani aiki kokuma saida wani abu a online, abunda ake so dakai kawai ta "Affiliate marketting" shine kawo customers su sayi wani abu a wani shafi na internet nawani kampani kokuma su kalli wani bidiyo, daga baya idan sun sayi wannan abun kai kuma za'a baka rabon ka. kamar dai yadda kaga dillalai sunayi wajen saida fili, gida, mota, kokuma wani abu makamancin hakan, kaima zaka iya zama dillali a internet cikin sauqi.
Kaji dadin darasin namu na yau?
indai har kaji dadin darasin mu na yau ka gaya mana a nan qasa kokuma kabi shafin facebook namu domin samun na gaba, ku kasance tare damu domin koyan wannan abubuwa kokuma taimako wajen koyar da su.
kuma kayi sharing zuwa groups guda uku kokuma zuwa shafinka na facebook. mun gode sosai.
TSOKACI: wannan darasin Gabatarwa neh kawai mukayi akan yadda ake kasuwanci kokuma samun kudi a yanar gizo. ku kasance tare da mu a darussa masu zuwa.
DARASI NA GABA: zamuyi magana akan "Content marketing"
Tags
Kommentarer