Fahimtar mafi muhimmanci daga cikin saitin Facebook (Facebook settings).
- Mustapha Ibrahim
- May 11, 2020
- 2 min read
Meyasa sanin “Facebook Privacy ya zama abu mai muhimmanci?
Idan ka maida “privacy” na facebook naka ya dawo “Public” Toh duk wanda yakeda account na facebook zai iya binciko kokuma ganin bayanai da suka shafi posts (rubuce-rubucen ka), and activity (da abubuwan da kake a facebook). Wanda yin hakan zai samu wata muhimmiyar rawa da zai taka a facebook account privacy ta hanyoyi masu yawa. Misali:
Mutane zasu iya ganin bayanai wanda suka kebance ka kokuma wanda bazaka so su gani ba a facebook, ba tare da sanin ka ba. Kamar irin su Ranar haihuwa, Adreshin gidan ka, lambar waya, da dai sauran su.
Duk abunda kayi pocting kamar comment (tsokaci) bidiyo, kokuma wasu abubuwa zasu iya zama a fili ga Mutanen da baka sani ba.
Posts da kayi wanda zasu iya zama abun kunya a gareka kokuma waninka zasu iya ganuwa ga kowwa da kowwa (kowwa zai iya gani)
Websites (shafukan yanar gizo) wanda muka fi sani da “Third-party websites” da kuma applications zasu iya gani kokuma su tura wasu bayanai muhimmai da Facebok account dinka (wanda suka shafe ka)
Hackers (Yahoo boys) zasu fi samun sauqin hacking facebook account naka.
Ka fahimci mafi muhimmanci daga cikin “Facebook privacy setting (saiti na sirri)"
Duk sadda ka tura wani abu akan facebook, Zaka iya zaban mutanen da kakeso suga wannan abun. A hoton da zamu bayar a nan qasa, zaku iya ganin settings irin su
Only me (Ni kadai), Lists (Nau’in mutane), Friends (Abokai), da kuma Public (kowwa da kowwa).
.

Yanzu kamar yadda kuke gani a wannan hoton a sama. Zamuyi bayanin ko wane daya daga ciki a nan kasa
· Only me: duk abunda zaka tura a facebook indai ka sashi a matsayin “only me” wato fassarar shi itace (Ni kadai) ma’ana kai kadai neh zaka ga wannan abubuwan indai ka saita shi a haka, toh komai ka tura a facebook babu wanda zai gani sai kai kadai.
· Lists: Shi kuma wannan zaka zaba mutanen da kakeso suga abubuwan da ka tura neh a facebook misali zaka iya zaban abokai da kake so suga wannan hoton, kokuma wannan bidiyon.
· Friends: Shi wannan saitin (settings) idan ka zabeshi a yayin da kake tura abubuwa a facebook kamar kana gayawa facebook neh cewa abokan ka kadai kakeso suga wannan abubuwan (bidiyo, audio, kokuma hoto).
· Public: Shi wannan saitin shine Oga kwata kwata, idan ka saita shi babu wanda bazai ga abunda kake turawa a facebook ba, amma kuma yafi had’ari domin za’a iya hacking account naka cikin sauqi, idan kanaso ka kiyaye facebook naka daga hacking sai ka danna nan, domin ganin yadda zaka kiyaye account naka babu wanda zai iya hackng nashi. Saidai ta hanyar "Phishing" wanda zamuyi bayani a nan gaba kadai kuma zamu koyar dashi ga subscribers namu kadai.
Da wannan neh Mukazo karshen darasin mu na yau Alhamdulillahi
Ku bibiye mu a www.Alfullaty.com domin samun shirye-shirye makamantan wannan da abubuwa masu dimbin yawa masu muhimmanci da zamu rika koyarwa a kan internet da kuma Degital marketing (wato koyan kasuwanci a internet).
Kada ku manta: Kuyi sharing (ku tura) wannan post din. Yin hakan zai taimaka min da kuma kara min karfin gwiwa wajen zuwa muku da sabbbin rubuce-rubuce da darussa masu amfani.
Za’a iya yin comment a nan kasa domin tambaya kokuma Karin bayani.
Na gode.
Tags
#Alfullaty #Facebook_settings #Facebook_privacy #Saitin_Facebook #Facebook_settings #Yadda_ake_facebook #Facebook #facebook_privacy_settings
Comments