
Facebook:
Sheikh Mubarak Alfullaty
Masanin Musulunci
RAYUWAR MAKARANTA
Sheikh Mubarak Ibrahim Alfullaty yayi karatu a wajen malamai da dama na musulunci, abun koyi neh ga matasa, ya kasance daya daga cikin matasa masu kishin Addini da kuma yada shi. SHeikh Mubarak yayi nasara wajen koyo da koyar da ilimin addini fannoni daban daban da suka hada da ilimin Al-Qur'ani, Hadisi, Fiqihu, tarihi, ilimin harshen larafci da adabin sa, da kuma ilimuka masu dinbin yawa.
Malaman sa sun hada da Sheikh Ibrahim Alfullaty da kuma Sheikh Ahmad Algarkawee kaduna.
AIKI / SANA'A
Malamin makaranta
Sheikh Mubarak Ibrahim Alfullaty shine mai gudanar da Makarantun Ibnu Qayyim Al-Jauziyyah .
kuma shi ne Ma'ajin kungiyar Shamsul Islam Organisation na yanzu da.
Malamin yayi nasara wajen rubuta littafai na Addinin musulunci wanda aka wallafa da kuma wanda ba'a wallafa ba
GUDUN MAWAR SA
Sheikh Mubarak Ibrahim Alfullaty tare da Sheikh Ibrahim Alfullaty, sune zasu jagoranci sashin "Addini" a cikin gidan yanar gizon, za a kara karatuttukan ta hanyar bidiyo da kuma audio (sauti) ta yadda zaku iya saukewa a wayoyin ku.
Latsa nan don ziyartar Shafin sa na Facebook.