top of page

Yadda ake tallata Kaya a Facebook.

A darasin da ya gabata, mun sake muku bidiyo akan yadda ake Bude shafin Facebook Domin kasuwanci, toh a yau zamu kawo muku sabon darasi akan yadda ake tallata Kaya a Facebook.


Idan baka kalli bidiyon daya gabata ba ka Danna nan, domin zuwa shafin YouTube namu na Mfullaty, a inda muka tanadar muku wannan bidiyon.

Ba tare da Bata lokaci ba zamu shiga cikin darasin kai tsaye.



Idan kanada kayan da kakeso ka tallata a shafin Facebook, toh ga wasu muhimman abubuwan da ya kamata ka kiyaye.


  1. Ka tabbatar kanada shafin Facebook: shafin Facebook yanada matukar muhimmanci wajen tallar abubuwan da dama, musammam ma idan kanada kayan saidawa, Kada ka yarda ka rika yin talla a Account dinka na Facebook, Sam hakan bai dace ba.

  2. Kasan mai zaka Rika posting: wannan ya hada da irin kayan da kake saidawa kokuma irin sana'ar ka, kada ka yadda ka tallata abunda bashi bane sana'ar ka a shafinka na Facebook, wannan babban kuskure neh.

  3. Kasan irin mutanen da zaka rika yiwa talla: Idan baka kula da irin customers naka, akwai yuyuwar ba irin mutanen da kakeso zasuzo shagonka ba balle su sayi abunda kake saidawa. misali: kana tallar littafai a shafin da ka saka mishi suwa "Furnitures", kaga a Nan bazaka samu irin customers da kakeso ba.

  4. Su waye mutanen ka?: Tabbatar mutanen da kake wa talla suna jin yaren da kake magana dasu. Bazai yiu ace kana Hausa ba, Amma turawa kake wa talla, kokuma kana turanci Amma Hausawa kake wa talla, hakan zaisa mutane su guji sana'ar ka.

  5. Abu na biyar shine ka samu yaddar jama'a: ta hanyar tabbatar musu da ingancin sana'ar ka da Kuma kyaun abunda kake sayarwa.


Idan kabi duk matakan da mukayi bayani a sama Ina tabbatar maka bakada wata damuwa a wajen tallar kasuwar ka kokuma sana'ar ka a Facebook.


Idan ka amfana da wannan darasin kayi share, zuwa wasu groups na WhatsApp da Facebook.

Mun gode.


Ku bibiye mu a sabuwar tashar mu ta YouTube, wato MFULLATY.


Darasi na gaba: Yadda zaka jawo mutane suyi liking shafin ka na Facebook.

 
 
 

Comments


  • Facebook

©All rights reserved @MFullaty.com

Alfullaty Technologies

NO.9 wambandiggi road, Albarka area maraba, Abuja Nigeria.

Contact

Thanks for contacting me, I will get back to you soon

bottom of page